Ba zan fasa yin Azumi ba saboda Tamaula – Mohamed Salah

Ba zan fasa yin Azumi ba saboda Tamaula – Mohamed Salah

Shahararen dan kwallon nan Muhammad Salah ya bayyana cewa duk da cewa yanzu lokacin azumi ne kuma ga wasan karshe na cin kofin zakarun turai bazai iya ajiye azumi ba saboda kwallon kafa.

Salah ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a shirye shiryen da kungiyarsa ta Liverpool tkeyi na buga wasan karshe da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a ranar Asabar.

A baya ana ta zuba ido ko dan wasan ya ajiye azumi a ranar Asabar saboda wasan na karshe domin ya samu kwarin gwuiwa da kuma karsashi a wasan da zasu fafata.

Ba zan fasa yin Azumi ba saboda Tamaula – Mohamed Salah
Ba zan fasa yin Azumi ba saboda Tamaula – Mohamed Salah

Sai dai rahotanni daga kasar Masar sunce dan wasan zaici gaba da yin azuminsa har zuwa ranar wasan kuma zai fita yayi wasansa batare da rashin karfi ba kamar yadda ake zato.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu

Wannan ba shine karo na farko da jarumin ke nuna jajirewa akan addininsa ba.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa zuwansa wani tsohon masallaci a Liverpool ya kara yawan mutanen dake halartar masallacin wanda ya hada da matasa da kuma tsofaffi, wanda ya kara daga martabar addinin musulunci a fadin kasar.

Dr. Abdul Hamid daya daga cikin malaman masallacin na Sheikh Abdullahi Quilliam yace matasa na ta kara tararowa masallacin suna gabatar da salloli a ciki harda sallar juma’a saboda Mohamed Salah, na zuwa masallacin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ga shafukanmu https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng