Dandalin kannywood: Rahma Sadau ta samu lambar yabo a matsayin jarumar jarumai na shekara
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa fitacciyar jarumar nan ta Kannywood, Rahama Sadau ta samu karramawa na musamman daga jaridar Leadership.
Ta samu lambar yabo a matsayin jarumar jarumai na wannan shekara. An kuma karramar jarumar ne a wajen bikin karrama fitattun yan Najeriya da suka kawo cigaba a kasar wanda aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.
An gudanar da bikin ne a daren ranar Alhamis, 24 ga watan Mayu.
Anyi bikin ne alhalin jarumar na kasar Cyprus saboda haka Uzee Usman ya wakilce ta.
Kamar yadda ta wallafa a shafin ta tare da hoton lambar yabon, Rahama Sadau ta nuna farin cikin ta da samun kyautar bayan an hada ta gasa da wasu fitattun jarumai.
KU KARANTA KUMA: Ragowar yarinyar Dapchi da ke hannun Boko Haram ba ta dawo gida ba har yanzu
Tayi ma dinbim masoyan ta godiya bisa goyon bayan da suke bata na yau da kullum wanda dashi take takama.
Daga karshe tayi ma jaridar Leadership godiya ta karramawar da suka bata tare da Uzee wanda ya amshi kyuatar a madadin ta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng