Ronaldinho ya kammala shirin auren mata 2 a lokaci guda a kasar Brazil
Sanannen abu ne cewa a kasar Brazil auren mata biyu a lokaci daya halastaccen lamari ne, wannan ne ya baiwa tsohon gwarzon dan kwallon Duniya Ronaldinho damar auren mata guda biyu a ranar daya, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ronaldinho ya kammala shirin auren yan matan nasa guda biyu, Priscilla Coalho da Beatriz Souza a watan Agustan shekarar 2018, inda a yanzu haka suna zaman lafiya tare a gidansa dake Rio De Janeiro, babban birnin kasar Brazil.
KU KARANTA: Na gamsu da zaman lafiyar da aka samu a Gambia – Buhari ga jakadan Gambia
Rahotanni sun tabbatar da cewar Ronaldinho ya fara soyayya da Beatriz ne a shekarar 2016, bayan shekaru tsawon shekaru yana tare da Priscilla, inda ya nemi aurensu a shekarar 2017, kuma ya siyan musu zoben aure iri daya.
Majiyarmu ta ruwaito a yanzu haka Ronaldinhi yana baiwa kowannensu pan 1500, kimanin naira 724,574.72 a matsayin kudin dawainiyarsu a duk wata.
Sai dai kanwar Ronaldinho wanda take adawa da auren matan guda biyu da zai ta ce ba zata halarci bikin aure nasa ba, amma a lokacin da kanwar Ronaldinho ta yi watsi da auren nasa, makwabcinsa kuwa, Jorge vercillo fitaccen mawaki ya dauki alwashin yin wasa a bikin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng