Bamu taba tattaunawa akan siyasar Buhari ko Atiku ko kuma wani dan siyasa da shekarunsa ya haura 70 ba – Kungiyar Arewa

Bamu taba tattaunawa akan siyasar Buhari ko Atiku ko kuma wani dan siyasa da shekarunsa ya haura 70 ba – Kungiyar Arewa

- Kungiyar matasan arewa wato CNG ta karyata fadin cewa kada‘yan siyasa da suka haure shekaru 70 su tsaya takara a shekarar 2019

- Kungiyar ta CNG ta bayyana goyon bayanta akan sake gina kasar, amma kuma da sharadin cewa wadanda zasu wakilci yankuna su kasance tsakanin shekaru 18 zuwa 60

- Kungiyar tace shawarar yin hakan itace domin dattawa dake jagoranci tun a shekarun baya su koma baya su bawa matasa wuri

Kungiyar matasan arewa wato CNG ta karyata fadin cewa kada‘yan siyasa da suka haure shekaru 70 su tsaya takara a shekarar 2019, lokacin da suka gana a garin kaduna kwanaki biyu da suka gabata, a Arewa House, domin tattaunawa akan muhimman abubuwa da suka shafi kasa, musamman na sake gina kasar.

Kungiyar ta CNG ta bayyana goyon bayanta akan sake gina kasar, amma kuma da sharadin cewa wadanda zasu wakilci yankin arewa a cikin wadanda zasu nemi takara su kasance tsakanin shekaru 18 zuwa 60.

Bamu taba tattaunawa akan siyasar Buhari ko Atiku ko kuma wani dan siyasa da shekarunsa ya haura 70 ba – Kungiyar Arewa
Bamu taba tattaunawa akan siyasar Buhari ko Atiku ko kuma wani dan siyasa da shekarunsa ya haura 70 ba – Kungiyar Arewa

Kungiyar tace shawarar yin hakan itace domin dattawa dake jagoranci tun a shekarun baya su koma baya su bawa matasa wuri.

KU KARANTA KUMA: Majalisa ta harzuka bayan ‘yan Sanda sun ce bincike akan satar sandar girma zai iya daukar shekara 10

Kungiyar tace taron sun gudanar dashi ne sakamakon korafi da ake ta kawo masu game da matsayinsu akan canza salon mulkin kasar, tun watanni shida da suka gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel