Ruwa baya tsami banza: An tsinci gawar wata mata kwanaki 7 da sallamar direbanta da Maigadi

Ruwa baya tsami banza: An tsinci gawar wata mata kwanaki 7 da sallamar direbanta da Maigadi

Wata mata mai suna Onise Ismail ta gamu da ajalinta a hannun wasu mutane da ba tabbatar da su ba, inda aka tsinci gawarta a gidanta dake rukunin gidaje na Citec, unguwar Mbora, kan babbar titn Jabi, a babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Punch ta ruwaito an tsinci gawar matar dauke da sara dayawa a kirjinta da wuyanta, inda a ranar Lahadin data gabata aka yi mata jana’aiza. Sai dai hankulan jama’a ya fi karkata ga wasu tsofaffin ma’aikatanta, wanda ta sallamesu daga aiki.

KU KARANTA: Matasa ci ma zaune: Buhari ma ci ma kwance ne – Inji wani Dan Najeriya da ya ji jiki

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar 14 ga wata Mayu ne miyagun mutane suka afka gidanta a lokacin da take kokarin tayar da Janareta, sai dai hakan ya faru ne kimanin kwanaki bakwai da mutuwarta, matar ta sallamai direbanta da Maigadinta.

Ruwa baya tsami banza: An tsinci gawar wata mata kwanaki 7 da sallamar direbanta da Maigadi
Matar

Wani dan uwanta ya bayyana ma majiyarmu cewa: “Mun samu labarin cewa makwabtanta suna jinta yayin da take magiya ga mutanen da cewa kada su kasheta, amma tsoro ya hana su kai mata dauki, don haka ko kafin mu gano ta, ta rigamu gidan gaskiya, kuma mutanen sun tsere.”

Zuwa yanzu hukumar Yansandan babban birnin tarayya Abuja ta kaddamar da binciken kwakwaf don gano masu hannu cikin kisan Onise.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel