Yanzu Yanzu: Mabiya addinin Katolika, maza da mata na gudanar da zanga-zanga a Lagas kan kisan da akeyiwa kiristocin a kasar (hotuna)

Yanzu Yanzu: Mabiya addinin Katolika, maza da mata na gudanar da zanga-zanga a Lagas kan kisan da akeyiwa kiristocin a kasar (hotuna)

Kasa da sa’o’i 24 bayan binne malaman addinin kirista biyu da wasu mambobin darikar Katolika da makiyaya suka kashe a jihar Benue, wasu kungiyar kiristoci sun fito zanga-zanga a jihar Lagas.

Zanga-zangar lumanan wanda Legit.ng ta dauko an gudanar da shine domin jan hankalin gwamnatin tarayya akan matakin da rashin tsaro ya kai a yankunan kasar da dama.

A wajen zanga-zangar akwai jami’an tsaro dake bincikar wadanda ke gudanar da zanga-zangar domin tabbatar da cewa an gudanar da gangamin cikin lafiya.

Yanzu Yanzu: Mabiya addinin Katolika, maza da mata na gudanar da zanga-zanga a Lagas kan kisan da akeyiwa kiristocin a kasar (hotuna)
Mabiya addinin Katolika, maza da mata na gudanar da zanga-zanga a Lagas kan kisan da akeyiwa kiristocin a kasar

KU KARANTA KUMA: Mahaifin budurwar da saurayinta ya kashe ya fadawa saurin nata cewa sai ya auri gawar diyar tasa

Mafi akasarin masu gangamin sun kasance mata dake korafin cewa a matsayinsu na iyaye mata suna jinjina lamarin tsaro a kasar wanda ya mayar da wasu zawarawa, ya maida yara marayu sannan kuma ya mayar da wasu marasa galihu.

Yanzu Yanzu: Mabiya addinin Katolika, maza da mata na gudanar da zanga-zanga a Lagas kan kisan da akeyiwa kiristocin a kasar (hotuna)
Mabiya addinin Katolika, maza da mata na gudanar da zanga-zanga a Lagas kan kisan da akeyiwa kiristocin a kasar

Yanzu Yanzu: Mabiya addinin Katolika, maza da mata na gudanar da zanga-zanga a Lagas kan kisan da akeyiwa kiristocin a kasar (hotuna)
Yanzu Yanzu: Mabiya addinin Katolika, maza da mata na gudanar da zanga-zanga a Lagas kan kisan da akeyiwa kiristocin a kasar

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa hawaye sun kwaranya yayinda aka binne shugabannin coci giuda biyu da wasu 17 da aka kashe a garin Makurdi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel