Gwamnatin Tarayya za ta fadada Shirin N-Power - Osinbajo

Gwamnatin Tarayya za ta fadada Shirin N-Power - Osinbajo

Majiyar mu ta samu rahoton cewa, gwamnatin tarayya ta kudiri aniyyar fadada shirin nan na N-Power a kasar nan domin kyautatawa matasan Najeriya da suka kammala karatuttukan su a fannikan nazari daban-daban.

Shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, shine yayi wannan sabon albishir ga matasan a ranar Juma'ar da ta gabata.

Osinbajo bayyana hakan ne yayin ziyarar wasu matasa dake cikin shirin na N-Power a harabar su ta koyan sana'o'I ta Kiara De-Luke dake garin Umuobiaka a karamar hukumar Obingwa ta jihar Abia.

Yayin gabatar da jawaban sa ga matasan, Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa shirin na N-Power yana da matukar muhimmanci ga gwamnatin tarayya a sakamakon akida da manufa ta karfafa madafa ta samun abin dogaro da kai ga matasa wajen horas da su sana'o'i.

Gwamnatin Tarayya za ta fadada Shirin N-Power - Osinbajo
Gwamnatin Tarayya za ta fadada Shirin N-Power - Osinbajo

Osinbajo ya ci gaba da cewa, a sakamakon haka ne gwamnatin tarayya ta kudiri aniyyar fadada shirin da kuma inganta shi wajen kara kaimi da hazakar matasa a masana'antun su.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Rundunar Sojin Kasa ta salwantar da rayukan 'Yan ta'adda 2, 11 sun shiga hannu

Ya kara da cewa, wannan wata dama ce ga matasa da ya kamata su rika da gaskiya da jajircewa bisa aiki da zata taimaka wajen gogayya da sauran matasa a duniya.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya jinjinawa mataimakin shugaban kasar dangane da tsayuwar dakan sa akan wannan shiri domin ganin cewa matasa sun yaki talauci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng