Akuyar mu ta je Amurka ta bada mamaki gaban Turawa
- Ana mamakin yadda akuya tayi wayau da gane mutane
- Turawa dai sun manta rayuwar kauye ko ta gona
- Yoga wata rayuwar motsa jiki ce wadda a zamanin da take kamar sallar wasu addinai

Wasu dalibai a Amurka sun shaku da wata Akuyar Najeriya kamar dai yanda ake shakuwa da dabbobin gida.

Daliban na wasannin motsa jiki tare da Akuyar Najeriya a wuraren da aka kebe don motsa jiki.

Wasannin na motsa ake gudanarwa yanzu a sassan kasar Amurka da Akuyar Najeriya.

Bayanai sun nuna cewa, tun 1950, kimanin shekaru 58 kenan da aka tafi da gajerun Awakin zuwa Amurka wadanda aka fi samu a kudancin kasar Najeriya. Amfanin Akuyar kuwa shine, samar da madara da kuma wasanni a gidaje sakamakon kankantarta.
Ga wasu hotuna masu nuna yanda ake wasannin da Akuyar Najeriya, a biranen Los Angeles da kuma California na kasar Amurka.
DUBA WANNAN: Zabukan Kaduna basu yi wani armashi ba
Turawa dai, ajebotas ne, duk wani abu da mu muka saba dashi a nan kamar banza, su a wurinsu, abu ne na ban mamaki, kuma yakan zamar dasu kauyawa.
Labari da Hotuna daga BBC Hausa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng