'Yar wasan kwallon kafa ta musulunta

'Yar wasan kwallon kafa ta musulunta

'Yan kasar Sweden wadanda suka yi kaurin sunan wajen kyamar Musulmi, sun razana matuka a lokacin labarin musuluntar Ronja Anderson, daya daga cikin kusoshin kungiyarsu ta kwallon kafa ta 'ya 'ya mata,U19 ya iso masu.

A wani jawabii da ta yi gaban manema labaran daya daga cikin jaridun da aka fi bugawa a Sweden, Afonbladet Anderson ta ce bayan ta karbi addinin Musulunci, 'yan uwa da aminnan arzikinta sun yi ta cuzguna ma ta tare da jifar ta da kalaman kiyayya,amma duk da haka tana alfaheri da kasancewa Musulma.

Anderson, kwararriyar mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta 'ya 'ya mata ta IK Uppsala ta kasar Sweden,ta sanar da cewa Musulmantarta ta yi tasiri sosai kan rayuwar kawayenta da dama.

Bugu da kari ta ce,"Sai bayan na Musulunta, na gane cewa yanzu ne na yi gamdakatar da kyaukyawan addini.Na yi imani da duk abin da Kur'ani ya zo da shi.A yanzu na san Allah,kuma ina ji a jikina irin tallafin da yake mun".

KU KARANTA KUMA: Sufeto janar na yan sanda ya bukaci ‘Yan Najeriya da su marawa Buhari baya game da yaki da rashawa

Misiz Anderson wacce a yanzu haka ta shaida cewa tana ci gaba da yin ka-in da na-in wajen ganin ta bi umarnin da Musulunci ya zo da shi sau da kafa,ta dauki alkwarin azumtar azumin watan Ramalana mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel