Hawaye sun kwaranya yayinda aka binne Marigayi Isyaka Rabiu a Kano (hotuna)
An yi Jana'izar marigayi Isyaka Rabi’u bayan Sallah Juma’a’a yau 11 ga watan Mayu.
An binne shi a cikin makabartar da ke cikin gidansa a Kano.
Manyan mutane da masu ruwa da tsaki a kasar sun halarci jana’izarsa ciki harda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.
Yawan cunkoson da aka smau a wajen binne marigayin ya sa wasu manyan masu fada a ji na Najeriya ba su samu shiga wajen da aka binne shi ba, ciki har da shahararren mai kudin nan, Aminu Dantata, da wasu manyan mutane.
Gwamnonin jihohin Neja da Jigawa da Kano ne kawai suka samu shiga, sai kuma 'ya'yansa da wasu daga cikin jikokinsa.
Manyan 'ya'yansa hudu ne suka saka shi a kabarinsa, wato Nafi'u da Abdussamad da Rabi'u (Alhaji Karami) da kuma Naziru.
Karin hotuna:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng