Gambiya ta sanya motoci da jirgin saman tsohon Shugaban Kasar Jammeh a kasuwa

Gambiya ta sanya motoci da jirgin saman tsohon Shugaban Kasar Jammeh a kasuwa

Gwamnatin kasar Gambiya ta sanar da yin gwanjon mota da jirgin sama mallakar tsohon Shugabanta Yahya Jammeh.

A yanzu mota da jirgin na kasuwa ga duk wanda ke bukatan ya saya.

Ministan Kudi na kasar ya bayyana cewa, an sanya motocin wadanda suka hada da samfurin Hummer Rolls Joyce a kasuwa.

Ministan ya kara da cewa, baya ga motocin akwai jirgin sama karami na musamman mallakar Jammeh wanda shi ma an sanya shi a kasuwa ga duk mai bukata.

Gambiya ta sanya motoci da jirgin saman tsohon Shugaban Kasar Jammeh a kasuwa
Gambiya ta sanya motoci da jirgin saman tsohon Shugaban Kasar Jammeh a kasuwa

An bayyana cewa, anyiwa motocin lamba da sunan Jammeh, matarsa da ‘ya’yansa.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya jawowa tsinannun Sanatoci ayoyin Al-Kur'ani

Jammeh dai ya mallaki manyan motoci tsadaddu sama da 10.

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF dai ya bayyana cewa, tattalin arzikin Gambiya ya fara farfadowa amma kuma ana bin kasar basuka da yawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng