Hana Fatauci Maganin Tari ba tare da tsauraran Matakai ba zai wadatar ba a Najeriya - JNI

Hana Fatauci Maganin Tari ba tare da tsauraran Matakai ba zai wadatar ba a Najeriya - JNI

A yayin da gwamnatin tarayya ta zartar da dokar hana fataucin maganin nan na Tari mai sunan Codeine a fadin kasar nan, kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta tofa albarkacin bakin ta cikin lamarin tare da bayar da shawarwari na matakan da ya kamata a dauka.

Kungiyar da sanadin babban sakataren ta, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, ta bayyana cewa hana fatauci da ta'ammali da maganin Codeine ba zai wadatar kadai ba muddin ba a gindaya tsauraran matakai da hukunce-hukunce ba.

Babban sakataren ya bayyana hakan ne yayin gudanar da taro na shirye-shiryen maraba da azumin Ramadana mai gabatowa a jihar Kaduna.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito Dakta Khalid ya bayyana cewa, dole gwamnatin tarayya ta gindaya tsauraran matakai doriya akan dokar hana fataucin muggan kwayoyi da za su magance wannan annoba a kasar nan.

Hana Fatauci Maganin Tari ba tare da tsauraran Matakai ba zai wadatar ba a Najeriya - JNI
Hana Fatauci Maganin Tari ba tare da tsauraran Matakai ba zai wadatar ba a Najeriya - JNI

Ya ci gaba da cewa, ya kamata a gindaya wasu matakai da hukunce-hukunce da za a zartar kan duk wanda aka cafke yayin sabawa wannan sabuwar doka inda ya bayar da misalin shekaru 10 a gidan kaso ba tare da zabi na bayar da beli ba domin ya zamto izina ga sauran al'umma.

KARANTA KUMA: Ashe wasu 'yan Majalisa da jami'an Tsaro suka hada tuggu na sace Sandar Majalisa - Hukumar 'Yan sanda

Jagoran kungiyar ya kara da cewa, ko shakka ba bu ta'ammali da muggan kwayoyi na daya daga cikin ababen dake rusa kasar nan inda ya bayyana mamakin sa dangane da yadda ake amfani da kwalabe kimanin miliyan uku na Codeine cikin jihar Kano da Jigawa kadai.

A yayin haka shugaban kwamitin tabbatar da da'a yayin gudanar da Tafsiri, Sheikh Tijjani Umaru, ya gargadi Malumma a kan kiyaye harsunan su yayin gudanar da Hudubobi, inda ya ce ire-iren munanan lafuza suka ta'azzara annobar Boko Haram a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel