Za'a hana shiga da na'urori da wayar salula fadar gwamnati a Najeriya
- Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya haramta amfani da wayoyi, laptop, ipads da kuma duk na'urorin daukar sauti a gidan gwamnati.
- Majiyar mu Legit.ng ta gano cewa hana amfani da na'urorin ya biyo bayan yaduwar dokokin da aka zanta a taron zababbun da akayi a jihar
Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya haramta amfani da wayoyi, laptop, ipads da kuma duk na'urorin daukar sauti a gidan gwamnati. Majiyar mu Legit.ng ta gano cewa hana amfani da na'urorin ya biyo bayan yaduwar dokokin da aka zanta a taron zababbun da akayi a jihar
DUBA WANNAN: Wenger yayi bankwana da Arsenal a jiya
An tabbatar da hanawar ne a jiya ta bakin babban mataimakin gwamnan akan tsaron cikin gida, Dr. Kenneth Ugballa.
"Daga yanzu wayoyi, laptops, ipads da na'urori masu mayen karfe an dena shigo cikin majalisar da ofishin gwamnan." inji mataimakin gwamnan.
Wakilin mu wanda yake a gidan gwamnatin lokacin da gwamnan yayi taro da shugabannin jami'ar jihar Ebonyi (EBSU), ya lura cewa 'yan majalisar jihar, da mataimakin gwamnan jihar, Dr Kelechi Igwe da manema labarai duk an hanasu shiga zauren majalisar da wayoyin su.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng