Turkiyya: Turawa mahaukata ne da suke kira ayi wa Al-Qurani kwaskwarima
- Kakakin Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalın ya bayyana cewa, daga nan har zuwa tashin alkiyama za aci gaba da tsare Alkur'ani Mai Tsarki.
- Turkiyya ta mayar da martani ga wasu 'yan siyasa marubuta su 300.
Kakakin Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalın ya bayyana cewa, daga nan har zuwa tashin alkiyama za aci gaba da tsare Alkur'ani Mai Tsarki.
Turkiyya ta mayar da martani ga wasu 'yan siyasa marubuta su 300.
DUBA WANNAN: Wani barawo yace ya saci wayoyi sama da 1200 a jihar Legas
Mutanen sun hada da tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy wadanda suka nemi da a yi wa Alkur'ani Mai tsarki gyare-gyare saboda sunce yana dauke da bayanan nuna kyama ga Yahudu da Nasara.
Kakakin na Shugaban kasar Turkiyya Ibrahim Kalın yace,
"Alkur'ani Mai Tsarki ba allon kowa da kowa ba ne na rubuta goge ba. Littafinmu ne Mai tsarki. Kuma daga nan har zuwa tashin Alkiyama za a ci gaba da tsare Shi. Kyamar Yahudawa wani tsarine da ya fito daga Turai. Kasashen Yamma da ke son magance wannan matsala to su tambayi Kasashensu. Wannan na nuna wauta da jahilci a zamanin yau."
Shi ma Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya mayar da martani ga 'yan siyasar na Faransa da cewa, "Wannan kalami nasu alama ce ta nuna kyama ga Musulunci. Sun wuce gona da iri. Idan aka yi irin wadannan kalamai me ya ke faru wa a Turai? Sai akai hare-hare kan Masallatan Juma'a."
Yace, a tsawon tarihi Kasashen Yamma sun zalunci Yahudawa. "Kun zalunci Yahudawa, Daular Usmaniyya da Jamhuriyar Turkiyya. Musulmai ne suka tsare su."
Cavusoğlu ya ci gaba da cewa, babu kyamar Yahudawa a wajen Musulmi. Hakan ya samawa imaninmu da Alkur'aninmu Mai Girma. Shin wa za ku ba wa darasi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng