Hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga jama'a su guji wadannan abubuwa

Hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga jama'a su guji wadannan abubuwa

- Anyi kira ga jama'a su guji kiba da maiko

- An mayar da kayan kwalam da makwalashe abinci

- Kiwon lafiya na farawa daga ciki ne

Hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga jama'a su guji wadannan abubuwa
Hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga jama'a su guji wadannan abubuwa

Hukumar lafiya ta duniya, tayi kira ga jama'a dasu guji kayan abinci masu sanya qiba, da taiba, kamar maiqo da zaqi, musamman ga wadanda basu essasaye wato motsa jiki.

An sami karuwar masu mutuwa sosai saboda sunki bin wannan shawara, musamman cikin matasa, a kuma kasashe masu tasowa, wadanda arziki yayi musu gwauron kamu. Ita dai hukumar a jiya ta fitar da sanarwar, ganin a shekara mutum 17m ke mutuwa daga kibar.

Abinci mai maiko kan sanya masu kin motsa jiki zama wuri daya tara mai watau kwalestarol a cikin jini, wanda shi kuma yana zuwa ne ya toshe jijiyoyi ya hana jini gudana yadda ya kamata.

DUBA WANNAN: Anso a kashe Theresa May ta Ingila

Abincina masu sanya qiba sun hada da siga, kwai, jan nama, kitse na dabba, bota na biredi, da ma kayan abincin da aka soya, musamman ga manya, illar tafi yawa.

A ci kayan ganye da abinci mai saukin siga, a ci kayan itatuwa, aci daga kayan gona ba na kanti ba, a ci a sha a kuma duba jini da ma motsa jiki, in ba haka ba, likita zai sami aboki da wuri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel