Ta'addanci: Dubi addu'o'i da Boko Haram keyi kafin su kai hari kan jama'a

Ta'addanci: Dubi addu'o'i da Boko Haram keyi kafin su kai hari kan jama'a

- Sun kwanta kamar gawa liman na musu sallah

- Su hudu ne da tsakar daren alhamis

- Wayar soja ta yi kuwwa sun tsere, washegari sun kai hari

Ta'addanci: Dubi addu'o'i da Boko Haram keyi kafin su kai hari kan jama'a
Ta'addanci: Dubi addu'o'i da Boko Haram keyi kafin su kai hari kan jama'a

A bayan jami'ar Maiduguri ne aka kyarawa sojoji cewa akwai alamun mayakan Boko Haram na rara-gefe domin kai hare-hare a ranar alhamis da ta wuce. Sojoji suka iso wurin suka yi kwanto, suna kallo ana yi wa wasu samari sallar gawa.

Samarin guda hudu, sun iso ne wajen biyun dare da tocila, sai wani dattijo ya iso, inda suka kwanta yayi musu sallar gawa, amma kafin ya gama sai wayar wani daga cikin sojojin ta yi ringing, kawai sai ja'iran samarin suka tashi suka tsere.

Duk da sojoji sun fara harbi, basu sami nasarar kama ko harbe kowa ba, inda suka ce duhu yayi yawa sosai.

DUBA WANNAN: Kemi Adeosun ta yi barnar kudi

A karshe sai suka je suka kwashe kayan da mayakan suka bari, waya, man fetur, kayan abinci a buhu da takalma.

A juma'a kuma, sai aka ji labarin harin mayakan Boko Haram su hudu a cikin birnin maiduguri, sun kashe mutane da dama.

A addinin Islama dai, ana iya yi wa wanda zai je jihadi da ake sa rai ba zai yi rai ba sallar gawa, kuma 'yan Boko Haram suna kiran kansu musulman asali masu koyi da irin abin da musulman farko suka yi, watau da'awa da kuma jihadi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel