Asin da Asin: Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo sun dunkule a jihar Legas
Tsohon shugaban kasa cif Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakinsa Alhaji Atiku ABubakar sun ci karo da juna a yayin taron tunawa da CIf Abraham Adesanya karo na 10, inda har suka zauna kugu da kugu, inji rahoton The Cables.
Marigayi Adesanya ya kasance tsohon dan gwagwarmaya dake nuna adawa da mulkin Soja kuma jigo a tafiyar maido da tsarin Dimukradiyya a Najeriya, NADECO, kuma a bana ne ya cika shekaru goma cur da rasuwa, hakan ta sanya iyalai da abokan arziki shirya taron tunawa da shi a duk shekara.
KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun kama wani kasurgumin dan bindiga a jihar Benuwe
A yayin wannan taro an hangi tsofaffin aminai, Atiku da Obasanjo suna gaisawa a dandalin Muson, sa’annan suka yi kus kus, daga bisani kuma aka hada musu wajen zama tare, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Idan za’a tuna, Obasanjo da Atiku sun kasance shugaban kasa da mataimakinsa tun daga shekarar 1999 zuwa 2007, sai dai danganta yayi tsami a tsakaninsu a karshen zangon mulkinsu, sakamakon rikici irin na bukata.
Sai dai sun shirya a lokutta daban daban, na baya bayan nan kuwa shine gab da zabukan 2015, inda hadakan yan siyasa suka kafa jam’iyyar APC, kuma suka samu goyon bayan Obasanjo da nufin kayar da tsohon shugaba Jonathan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng