Karin albashi: Wasu Gwamnoni sun fara sa alamar tambaya tun kafin a je ko ina

Karin albashi: Wasu Gwamnoni sun fara sa alamar tambaya tun kafin a je ko ina

Kwanan nan aka yi bikin ranar kwadago ta Duniya inda ku ka ji cewa maganar karin albashin Ma’aikata a Najeriya yayi karfi. Wasu Gwamnoni dai sun fara nuna cewa fa da kyar za su iya biyan Ma’aikatan su albashin N65000 duk wata.

Ko da dai Jihohi da dama su na fama da matsalar biyan albashin da bai wuce N18000 ba, don haka daidaikun Jihohi ne za su iya biyan Ma’aikatan su abin da ya kai N56000 zuwa N65000. Tuni wasu Gwamnonin sun fara kokawa.

Karin albashi: Wasu Gwamnoni sun fara sa alamar tambaya tun kafin a je ko ina
Wike ya nemi a banbanta albashin Ma'aikata a Najeriya

Jihohi da dama dai ba za su iya biyan wannan kudi ba amma dai wasu sun fara kokawa tun yanzu. Ga dai jerin Gwamnonin nan kamar haka:

KU KARANTA: Wani Gwamna ya nemi a bi a hankali game da batun karin albashi

1. Gwamnan Jihar Bauchi

Gwamna Mohammed Abubakar na Jihar Bauchi yace sam ba zai iya biyan Ma’aikatan Bauchi N65000 ba saboda kudin shigan Jihar da abin da Gwamnatin Tarayya ta ke badawa bai wuce Biliyan 8 ba yayin da yake biyan albashin Biliyan 5 a yanzu haka.

2. Gwamnan Jihar Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina bai ce ba zai iya biyan albashi idan aka kara ba amma dai ya nuna cewa karin albashin ba zai zama mafita ba don kuwa ko an kara albashi idan ba a duba harkar ilmi da sauran su ba, komai zai sake cabewa a Kasar.

3. Gwamnan Jihar Ribas

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas yace bai dace ace za a daidaita mafi karancin albashi a ko ina a fadin kasar ba saboda wasu Jihohin sun fi wasu arziki. Jihar Ribas na cikin mafi arziki a kasar amma dai Gwamna Wike ya fara nuna akwai gyara a maganar tun yanzu.

Ku na da labari cewa Majalisar Wakilan Tarayya tace a shirye ta ke tayi na’am da kudirin kara albashin Ma’aikata da zarar ya zo daga fadar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel