Shehu Sani ya bayyana halin da ya tsinci Dino Melaye

Shehu Sani ya bayyana halin da ya tsinci Dino Melaye

Wakilin al’ummar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani ya bayyana halin da ya tsinci Sanata Dino Melaye a Asibiti, inda yace sanatan na cikin mawuyacin hali, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sani na daga cikin tawagar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki da suka kai ma Dino Melaye ziyara a babban Asibitin kasa a ranar Laraba, don haka ne ma Sani yace ba shi da tabbacin ko Dino a sume yake ko kuwa a farke.

KU KARANTA: Muhimman ayyuka guda 6 da Atiku Abubakar ya lashi takobin aiwatarwa idan ya zama shugaban Najeriya

“Sun cire ankwar dake hannunsa, amma suna yi masa karin ruwa, baya iya magana, kuma akwai katon bandeji a wuyarsa, nib a likita bane balle na fahimci halin da yake ciki na nufin farfadowa ko akasin haka.” Inji shi.

Shehu Sani ya bayyana halin da ya tsinci Dino Melaye
Dino Melaye

Melaye ya tsinci kansa cikin wannan halin ne tun bayan daya diro daga wata motar Yansanda yayin da suke kan hanyar zuwa Lokoja na jihar Kogi don halartar zaman Kotun da Yansanda suka kai shi kara kan wasu tuhume tuhume da suke masa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito bayan da Sanata ya tsere ne daga hannun Yansanda ya samu rauni, jama’ansa suka kai shi wani Asibiti mai zaman kansa, daga bisan Yansanda suka bi shi can, suka sake cafke shi, inda suka garzaya da shi zuwa bababn Asibiti daure cikin ankwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: