Mawakin da ya yi wakar cin zarafin Allah da manzon sa a Kano ya shiga hannu
- A kwanakin baya ne wani mawaki da ba a san ko waye ba ya wallafa wata waka ta cin zarafi ga Allah da manzon sa
- Hukumar Hisba, ta bakin shugaban ta; Aminu Daurawa, ta ce ta kama mawakin
- Daurawa ya bayyana hakan ne a jiya Asabar da daddare a wurin wa'azi da kungiyar Izala ta gudanar a Kano
A kwanakin baya ne wani mawaki da ba a san ko waye ba ya wallafa wata waka dake cin zarafin Allah da manzon sa.
Al'ummar musulmi sun nuna rashin jin dadin su da bacin rai bisa kalaman dake cikin wakar.
Hukumar HISBA, ta bakin shugaban ta, Aminu Ibrahim Daura, ta ce ta kama wanda ya wallafa wakar.
Daurawa ya bayyana hakan ne a daren jiya, Asabar, yayin gudanar da wa'azi da kungiyar Izala ta shirya a jihar Kano.
DUBA WANNAN: Auren jinsi: Buhari ya mayar wa da Firaministar Ingila martani
Ko a wasu shekaru da suka wuce saida aka samu hargitsi a garin Kano biyo bayan wasu kalamai na gatsali da shirka ga Allah da manzon sa da wasu mabiya darika suka yi.
Daurawa ya ce zasu gurfanar da mawakin da duk wadanda keda hannu cikin buga wakar da yada ta a gari domin girbar abinda suka girba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng