Sannu sannu bata hana zuwa: Cikin naira biliyan 4, EFCC ta kwato naira miliyan 473 daga hunnun jigon APC

Sannu sannu bata hana zuwa: Cikin naira biliyan 4, EFCC ta kwato naira miliyan 473 daga hunnun jigon APC

Hukumar yaki da rashawa, da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta sanar da kwato naira miliyan dari hudu da saba’in da uku, (473) daga cikin naira biliyan hudu da miliyan sittin da takwas (4.68bn) da ake tuhumar wani jigo a jam’iyyar APC, da kuma wani tsohon gwamna suka sata.

EFCC ta zargi tsohon ministan Jonathan, Musliu Obanikoro, wanda jigon ne a jam’iyyar APC da tsohon gwamnan jihar Osun, Iyiola Omisore da laifin raba naira biliyan 4.68 a gabanin zaben gwamnan jihar Osun, da nufin tafka magudi da aringizo a yayin zaben.

KU KARANTA: Aikata baɗala a gidajen kallon kwallo: Sarkin Kano ya baiwa Daurawa muhimmin aiki

Daily Trust ta ruwaito hukumar EFCC ta samu nasarar kwato makudan kudaden daga hannun wadanda ake zargi a yayin da ta kammala shirye shiryen gurfanar da wadanda take tuhuma gaban kuliya manta sabo.

Sannu sannu bata hana zuwa: Cikin naira biliyan 4, EFCC ta kwato naira miliyan 473 daga hunnun jigon APC
Omisore da Obanikoro

Majiyar Legit.ng ta ruwaito EFCC ta kwato naira miliyan 350 daga cikin naira biliyan 1.7 da gwamnatin Jonathan ta baiwa Omisore ta hannun Obanikoro don ya sake tsayawa takara a zaben gwamnan jihar Osun.

Yayin da hukumar ta kwato naira milyan 123 daga hannun Obanikoro, wanda yace tsohon mashawarcin Goodluck Jonathan kan sha’anin tsaro, Sambo Dasuki ne ya umarce shi ya kai ma Omisore kudaden, shi dan aike ne kawai, inji shi.

Binciken hukumar EFCC ya tabbatar da cewar Sambo Dasuki ya baiwa gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose zambar kudi naira biliyan 1.3, sa’annan ya kara masa dalan Amurka miliyan 5, duk don gudanar da yakin neman zaben gwamna a shekarar 2013.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel