An kashe maciji ba’a sare kansa ba: Yaran Buharin Daji sun hallaka wasu mutane 2 a jihar Zamfara
Wasu yan bindiga da ake zargin yaran tsohon kasurgumin dan fashin nan ne da ya addabi jihar Zamfara, Buharin Daji sun bindige wasu mutane guda biyu har lahira ba cas ba as, inji rahoton Rariya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun yi ma mutanen kisar gillar ne yayin da suke kan hanyar kauyen Kabaro dake tsakanin garin Bena da Dansadau, duk a cikin karamar hukumar Maru ta jihar.
KU KARANTA: Hargitsi a majalisar dattawa: Jami’an Yansanda sun kwato ‘Sandar Iko’ da ɓarayi suka sace
Rahotanni sun tabbatar da cewar maharani sun hallaka wani mai suna Abdullahi mai kifi ne ta hanyar bindige shi, sa’annan suka yi masa yankan rago, daga bisan kuma suka isahe Malam Shehu Badakkare, inda suke murde masa wuya sakamakon kasa kashe shi da bindiga.
Sai da majiyar ta ruwaito zuwa yanzu an yi ma mamatan jana’iza a babban asibitin garin Dansandau. Tsaro ya kara tabarbarewa a Zamfara tun bayan kisan Buharin Daji da wani tsohon Yaronsa yayi.
Inda ko a kwanakin baya sai da yaran Buharin suka shiga jihar Kaduna, inda suka bindige wasu Sojoji guda goma sha daya dake jibge a wani kauyen Birnin Gwari.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng