Rikicin Majalisa: Gwamnatin Najeriya ta nemi ayi binciken gaggawa
- Gwamnatin Tarayya ta bada umarni a binciki abin da ya auku jiya a Majalisa
- Bayan nan kuma Mataimakin Shugaban kasa ma ya jajantawa ‘Yan Majalisar
- Gwamnati za ta kara Jami’an tsaro a Majalisa domin gudun a maimaita gobe
Mun samu labari daga manema labarai cewa Gwamnatin Tarayya ta yi mamakin abin da ya faru a Majalisar Dattawa a jiya inda wasu tsageru su ka shiga har harabar Majalisar su kayi ta’asa.
Gwamnati ta yi maza-maza ta bada umarni a duba lamarin da ya ja aka sungume sandar girman Majalisa a Ranar Laraba. Fadar Shugaban kasar ta yi tir da wannan abu inda tace za ayi bincike kuma a hukunta wanda su kayi wannan mugun aiki.
KU KARANTA: Da sa hannun Shugaba Buhari wajen sungume sandar Majalisa - Fayose
Ministan yada labara na kasar Lai Mohammed ya bayyana cewa an ba Jami’an tsaro umarni su yi bincike game da lamarin aka kuma yi alkawarin za a kara Jami’an tsaro a Majalisar domin gudun aukuwar wannan mummunan ta’asa nan gaba.
Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya taya ‘Yan Majalisa jimamin wannan abu da ya faru. A jiya da yamma dai, Mataimakin Shugaban kasar ya gana da Mataimakin Shugaban Majalisa Dattawa Ike Ekweremadu da kuma Ita Enang.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng