Shin ana iya ganin waliyyai da gaske bayan sun mutu, Ko kuwa matsalar kwakwalwa ce?

Shin ana iya ganin waliyyai da gaske bayan sun mutu, Ko kuwa matsalar kwakwalwa ce?

- Soyayyar Shehu ta kai ana ganinsa a sama ko a fitila

- Ko a Iran ana iya ganin Khomeini a fuskar wata

- Kiristoci ma suna ganin Yesu a bango, ko a gasasshen biredi

Shin ana iya ganin waliyyai da gaske bayan sun mutu, Ko kuwa matsalar Kimiyya ce?

Shin ana iya ganin waliyyai da gaske bayan sun mutu, Ko kuwa matsalar Kimiyya ce?

A taron maulidi na Sheikh Ibrahim Inyass da aka yi a makon jiya a Abuja, an sami ganin Shehu a jikin fitila, inda jama'a suka yi ta turuwar sumbatar fitilar wai don anga Inyas a sama.

Manyam Maliman darikar Tijjaniyya dai sunce wannan tana daga cikin karamar Shehun, inda har ma aka danganta ruwan sama da aka samu a ranar da cewa karamar sa ce.

DUBA WANNAN: Malamai 12,000 sun kama aiki a Kaduna

Sai dai abin da basu lura ba, shine, hotunan Shehun waliyyin sun karade ko'ina a wurin taron, duk inda ka waiga sune, don haka bayan kallon hoton yini biyu, ko ina ka waiga kwakwalwarka tana iya nuna maka hoton sai kaga kamar sh din ne a wurin.

Misali, in ka qura wa rana ido, ka kuma kalli gefe, zaka ga dodon hoton ranar kamar yana kallonka a na wasu sa'o'i. Shi yasa da mutum na farko ya fadi, sai a kama rububi, shikenan, karama!

Shin ana iya ganin waliyyai da gaske bayan sun mutu, Ko kuwa matsalar Kimiyya ce?

Shin ana iya ganin waliyyai da gaske bayan sun mutu, Ko kuwa matsalar Kimiyya ce?

Hakan yana faruwa ga dukkan mai son wani abu ko ba Shaihu bane, musamman na wasu mutane da ake yayi.

A Iran, akan dauka in mutum bai ga hoton Khomeini a kan wata ba, ana ganin zunubbansa sunyi yawa. Haka a wurin masu son Yesu ko Maryama, suna ganin hotonsu. Ana ganin sunan Allah a Hadari, ko sunan annabi a kabewa.

Shin ana iya ganin waliyyai da gaske bayan sun mutu, Ko kuwa matsalar kwakwalwa ce?

Shin ana iya ganin waliyyai da gaske bayan sun mutu, Ko kuwa matsalar kwakwalwa ce?

A kasar Indiya, jama'a suna mafarki ko gani-ganin gumakansu, musamman giwarnan mai kama da mutum, watau Ganesha, in aka haifi da mai hannaye ko kafafu da yawa kuma sai a ce Alliya Nargis ce ta bayyana, ayi ta zuwa kwasar tunarraki, iyayenta suyi kudi...

Amma fa babu maganar a kai 'yar asibiti domin saukaka mata cutar da hanyen kan jawo, balle ace wai ko za'a yanke su tunda tagwaye ne dayar ta shiga daya tun suna ciki.

Duk dai wannan kawai shaci fadin masu chanfi ne, inda sukan ga wanda zukatan su ke so. Amma a zahiri, babu wanda zai iya tabbatar da wannan, saboda abin na masu ladabin soyayya ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel