Nigerian news All categories All tags
Ministar Buhari ta yi karin haske kan badakalar kudaden Abacha

Ministar Buhari ta yi karin haske kan badakalar kudaden Abacha

- Kemi Adeosun ta karyata rahoton cewa aika wasika ga Buhari wajen nemar dakatar da biyan lauyoyi

- Ta jadda cewa an kasa kudaden a wani asusu na musamman a CBN

Rahotanni sun kawo cewa ministar kudi, Kemi Adeosun ta wanke kanta daga zargi da ake yi mata.

An dai yi rahoton cewa Kemi ta aika wasika ga shugabna kasa Muhammadu Buhari inda ta bukaci a tsayar da biyan dala miliyan 16.9 ga wasu lauyoyi da suka taka rawa gani wajen dawowaa Najeriya da sama dad ala miliyan 322.

Wadannan kudade da suka dawo da su sun kasance na badakalar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, wato marigayi Sani Abcha, inda ya boye su a bankin kasar Swiss.

Ministar Buhari ta yi karin haske kan badakalar kudaden Abacha

Ministar Buhari ta yi karin haske kan badakalar kudaden Abacha

Ministar ta jaddada cewa a ranar 18 ga watan Disamba na shekarar 2017, gwamnatin kasar Swiss ta sanya wadannan kudade a cikin wani asusu na musamman da ke Babban Bankin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Tafiyan Landan: Dalilin da yasa Buhari bai rubuta wasika ga majalisar dokoki ba

Ana dai zargin Ministan Shari'a, Abubakar Malami da makarkashiyar yin amfani da lauyoyin wajen samun wani kaso daga kudaden na Abacha.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel