Duk inda dan kwallon Liverpool Mohammed Salah zaije da Kur’ani yake zuwa don karantawa (hotuna)
Mohammed Salah shahararren dan wasan nan na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ya kasance mutun da baya hada addininsa da komai, hakan yasa mutane da dama ke sha’awarsa fiye da abokan harkansa.
Har ila yau jarumin kwallon kafan kan dauki littafi mai tsarki a tare das hi a koda yaushe domin karantawa.
Lokuta da dama akan ga jarumin yayi sujadda a filin kwallo domin nuna godiyansa ga Allah musamman a lokutan da yayi nasarar jefa kwallo a raga.
Babu shakka ga dukkan alamu karatun Kur’anin yana daga cikin abubuwan dake ba jarumin sa’a tare da karfafa masa da samun nutsuwa a zuciyarsa.
KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya haura kasashen Duniya 17 domin ya je aikin Umrah
Abaya Legit.ng ta ruwaito cewa, Magoya bayan kungiyar, wanda yawancinsu Turawa ne sun nuna sha’awar addinin Musulunci saboda Mohammed Salah, inda wasu daga cikinsu ma suke ganin tamkar da’awah yake yi a cikin Fili.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng