Najeriya ta gargadi majalisar dinkin duniya kan hatsarin da ke tattare da malakar makamen kare dangi

Najeriya ta gargadi majalisar dinkin duniya kan hatsarin da ke tattare da malakar makamen kare dangi

Gwamnatin Najeriya tayi gargadi akan yadda har yanzu akwai kasashen duniya masu cigaba da ajiye makaman kare dangi wadanda akayi itifaki cewa barazana ce ga rayurwar al'ummar duniya baki daya.

Najeriya ta fadin hakan ne a wata sanarwar data bayar yayin mahawarar da akayi a majalisar dinkin duniya ta bakin sakataren janar mai wakiltar Najeriya, Faisal Ibrahim.

Sanarwan ta cigaba da cewa kudadin da ake kashe wa wajen kulawa da makaman da ingantasu yana da matukar yawa idan akayi kwatanta shi da kudaden da kasashe ke warewa wajen inganta rayuwar al'umma.

Najeriya ta gargadi majalisar dinkin duniya kan hatsarin da ke tattare da makamen kare dangi
Najeriya ta gargadi majalisar dinkin duniya kan hatsarin da ke tattare da makamen kare dangi

KU KARANTA: Kotu ta wanke dan Gaddafi daga zargin aikata kisa

"Akwai hanyoyi masu amfani da zasu taimakawa al'umma wajen cigaba da kara wanzar da zaman lafiya da ya dace a mayar da hankali a kai," inji sanarwan

Kazalika, sanarwan tayi tsokaci kan matsayar da kotun kasa da kasa ta bayar kan batun inda ta tabbatar da cewa barazana ko kuma amfani da makaman kare dangi laifi ne ga bil-adama.

Najeriya ta kuma jadada cewa matsayar na kotun kasa da kasa ya nuna cewa malaka da kuma amfani ko barazanar amfani da makaman kare dangin ya sabawa dokar kasa da kasa da ma dokar kare hakkin bil-adama.

Ta kuma janyo hankali kan irin fitinar da zai iya faruwa idan akayi amfani da makaman da gangan ko kuma aka samu kuskure makaman suka fashe, a cewar ta, wannan kadai dalili ne da zai ka sauran kasashen suyi watsi da makaman kare dangin nasu.

Najeriya tace zata cigaba da bayan da goyon bayan amfani da fasahar nukiliya wajen samar da ababen more rayuwa kamar lantarki da sauran su amma bata goyon bayan amfani dashi wajen kera makaman kare dangi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164