Kashe-Kashe: Gwamnan Zamfara ya ba da umurnin harbe duk wanda aka gani da makami
Gwamnan jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin kasar Alhaji Abdulaziz Yari ya bayar da umurni ga jami'an tsaron kasar musamman ma wadanda suke a jihar sa inda ake ta kashe-kashe cewar su harbe dukkan wani farar hula da suka gani rike da makami.
Haka ma Gwamnan ya kara da cewa su ma dukkan masu garkuwa da mutane ko kuma masu bayar da wurin boye su su ma a kashe su da agan su ba tare da wata-wata ba.
KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe wani jigon APC
Legit.ng ta samu cewa Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne a yayin wata ziyarar jaje da ya kai wa Sarkin Anka na jihar inda a kasar sa aka samu wasu 'yan binga da suka je wani kauye suka kashe mutane sama da 30.
A wani labarin kuma, A cikin wani yanayi mai cike da ban tausayi mai kama da shasshekar kuka, Sarkin masarautar Anka ta jihar Zamfara Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad ya yi kira ga majalisar dinkin duniya da tarayyar turai da su kawo wa jama'ar sa agajin gaggawa.
Sarkin ya ce yanzu kam dai ya zama wajibi ya nemi taimakon al'ummar duniya don ganin an kawo karshen kisan kiyashin da yan bindiga da ake kyautata zaton barayin shanu ne suke yi wa jama'ar sa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng