An gurfanar da wani mutun bisa zargin lalata nakasashiyar yarinya

An gurfanar da wani mutun bisa zargin lalata nakasashiyar yarinya

Wata kotun majistare dake Ikorodu taa ba da umurnin garkame wani mutumi mai shekaru 22 bisa zargin lalata wata nakasashiyar yarinya mai shekaru 12 wacce ta kasance yar makwabtan shi.

A cewar dan sanda mai kara, Iberedem, Folorunsho Galadinma na fuskantare tuhuma a kotu kan zargin yin lalata.

Iberedem ya fada ma kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin a ranar 15 ga watan Fabrairu da misalin karfe 7 na yamma a Prince Omodenye St., Ibefun, garin Owode dake Ikorodu.

An gurfanar da wani mutun bisa zargin lalata nakasashiyar yarinya
An gurfanar da wani mutun bisa zargin lalata nakasashiyar yarinya

Iberedem yace mai laifin ya saci hanya inda ya shiga gidan su yarinyar lokacin da mahaifiyarta ta fita debo ruwa.

“Ya yi lalata da yarinyar wacce ta kasance kurma amma mahaifiyar yarinyar ta kama shi a lokacin da yake aikata ta’asar.

KU KARANTA KUMA: Amfanin zogale 10 a jikin dan adam

“Ta nemi doki sannan wasu makwabta suka kama mutumin.” Laifin ya sama ma sashi na 137 na dokar jihar Lagas na 2015.

Mai shari’a, Misis F.A. Azeez ta daga sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Afrilu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng