Ban fadawa kowa lokacin da zan yi aure ba – Rahama Sadau

Ban fadawa kowa lokacin da zan yi aure ba – Rahama Sadau

Rahama Sadau tayi amfani da shafin sa na Tuwita ta bayyana cewa ba tayi hira da Legit.ng ba bayan da aka buga labari game da ita inda tace ba yau aka saba yi mata sharri.

Labari ya zo mana cewa fitaccen ‘Yar wasan kwaikwayon Najeriya Rahma Sadau ta musanta cewa tayi karin haske game da lokacin da za tayi aure.

Ban fadawa kowa lokacin da zan yi aure ba – Rahama Sadau
'Yar wasan Hausa Rahama Sadau tace ana yi mata sharri

‘Yar wasan fim din ta musanya cewa tayi hira da Legit.ng game da masoyan ta da kuma lokacin da za ta tare a gidan mijin ta. Dama a lokacin ta musanya cewa tana soyayya da babban Jarumin ‘Dan wasan Najeriya Ali Nuhu.

KU KARANTA: Rahama Sadau ta bayyana wanda za ta aura

Rahma Sadau ta bayyana mana cewa kusan sau uku kenan ana buga labarai a kan ta wanda duk ba ta fadi hakan da bakin ta ba. Babbar ‘Yar wasan ta Nollywood tace ana kirkikar labarai ne da gan-gan a kan ta cikin ‘Yan kwanakin nan.

A rahoton baya kun ji cewa Jarumar Hausar ta bayyana cewa dukkan mace za ta so ta auri namiji irin Ali Nuhu musamman ma saboda mutum ne nagari, mai tausayi da kyautatawa wanda kuma su ne siffofin da duk wata mace ke nema.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng