Yan matan Dapchi: Buhari ya nuna shi nagartaccen shugaba ne - Okorocha

Yan matan Dapchi: Buhari ya nuna shi nagartaccen shugaba ne - Okorocha

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana sakin yan matan Dapchi da yan Boko Haram suka sace a jihar Yobe a matsayin nagartaccen shugabanci a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wani jawabi da yayi ga manema labarai a Owerri tab akin babban sakatarensa, Mista Onwuemeodo, Okorocha yace wannan dalili shine abunda zai sa yan Najeriya su marawa Buhari baya.

Jawabin ya zo kamar haka: “Da dawowar yan matan makarantar Dapchi 104 bayan an shafe kwanaki 30 da sace su, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna siyasa mai karfi saboda yadda ya dauki lamarin a matsayinsa na shugaban kasa wanda hakan ya nuna karfin shugabancin sa."

Ya ci gaba da cewa: “Dawo da yan matan da akayi cikin gaggawa ya nuna jajircewar shugabancinsa saboda ba don jajircewar nasa ba toh da labara ya sha bambam a yanzu.”

KU KARANTA KUMA: Babu abin da ya dame ni da surutun wani can don ni ne Gwamna - Yahaya Bello

A halin da ake ciki, al’umman garin Dapchi na jihar Yobe sun jaddada cewa bazasu taba rabuwa da tabon sace yayansu da yan ta’addan Boko Haram sukayi ba idan ba wai an dawo da Leah Sharubu bane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng