Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki yan matan Dapchi

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki yan matan Dapchi

-Labari da duminsa, Boko Haram ta saki dukkan yan matan Dapchi

Labarin da ke shigowa yanzu daga majiyarmu na tabbatar mana da cewa cewa yan kungiyar Boko Haram sun saki yan matan Dapchi.

Rahoto ya kara da cewa sun mayar da su garin Dapchi amma an samu karamin akasi, biyar daga cikin yan matan sun rasa rayukansu.

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki yan matan Dapchi
Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki yan matan Dapchi

Shugaban kwamitin iyayen yan matan Dapchin, Bashir Manzo, ya tabbatar da cewa an daow da yan matan Dapchi.

"Iyalaina da abokan aiki sun sanar da ni cewa an dawo da yan matan da safen nan.

Ina hanya zuwa Dapchi yanzu daga Damaturu. Idan na kai zan kirgasu domin tabbatar idan dukkansu ne."

KU KARANTA: Yadda Sanata Dino ke loda mana kudi sannan yana siya mana bindigogi – ‘Yan ta’adda

Zamu kawo muku cikakken rahoton.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel