Buhari ya kure adaka; ba zai iya abin da ya wuce wannan ba - Shettima Yarima
- Matasan Arewa sun hurowa Shugaba Buhari wuta ya hakura da mulki
- Kungiyar AYCF tana ganin Shugaban ya gaza a tsaro da samar da aiki
- Shettima Yarima ya nemi Shugaban kasar ya mikawa wani mulki a 2019
Shugaban Matasan Yankin Arewa karkashin lemar AYCF sun hurowa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wuta da ya sauka daga mulki saboda ganin shekarun sa sun yi nisa da kuma fama da yake yi da rashin lafiya.
Shettima Yerima wanda shi ne Shugaban AYCF na Matasan Arewa masu neman ganin cigaban Yankin yace ya kamata Shugaba Buhari ya hakura ya ba wani matashi mulkin Kasar a wata hira da yayi da Sahara TV kwanan nan.
KU KARANTA: Najeriya na bukatar Arewa - Inji kungiyar AFC
Yerima yace Gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza wajen samawa Jama'a aikin yi da kuma harkar tsaro yayin da Shugaban kasar yake yawan halartar bukukuwa. Shugaban Matasan yace da Gwamnatin tana aiki da ba ayi ta samun kashe-kashe ba.
Wannan Bawan Allah yana ganin cewa Shugaba Buhari yayi bakin kokarin sa ganin irin larurar sa don haka ya kamata tun da mutunci ya yafe maganar sake neman takara a 2019 ya mikawa wani mai jini a jika ya karba daga inda ya tsaya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng