Mamora yaki karban sabuwar mukamin da Buhari ya bashi

Mamora yaki karban sabuwar mukamin da Buhari ya bashi

- Mamora ya raina sabuwar mukamin da Buhari ya bashi

- Sanata Mamora ya ce mukamin da shugaba Buhari ya bashi ya yi mishi kadan

Wani tsohon dan majalissar dattawa, kuma na kusa da shugaba Buhari, Sanata Olurunnimbe Mamora, yaki karban mukamin shugaban hukumar cibiyar harkokin kasuwanci na Abuja (AIIC) da Buhari ya nada shi.

Sanata Olurunnimbe Maomora, shine yayi mataimakin daraektan kamfen din shugaba Buhari a zaben 2015.

Jaridar SUNDAY PUNCH ta rawaito cewa, tsohowar ‘yar takaran gwamnan jihar Ondo a 2016 karkashin jam’iyyar APC, Misis Jumoke Ajasin Anifowoshe, aka nada a matsayin shugaban hukumar AIIC a makonni biyu da suka gabata.

Ministan Abuja, Alhaji Muhammad Bello, ya rantsar da ita a matsayin shugaban hukumar.

Mamora yaki karban sabuwar mukamin da Buhari ya bashi
Mamora yaki karban sabuwar mukamin da Buhari ya bashi

KU KARANTA : Rikicin Jam'iyyar APC ta Kaduna: Tsohon dan takarar Gwamna, Haruna Saeed ya fice daga jam’iyyar APC

Legit.ng ta samu rahoton cewa, Sanata Mamora ya fadawa Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, cewa bai ji dadin mukamin da aka bashi ba, saboda yayi mishi kadan.

Yayi korafin cewa, Mutanen da basu taimaka wa shugaba Buhari da komai ba a lokacin yakin neman zaben 2015 ne suke cin gajiyar gwamnatin sa..

Wani majiya mai karfi ya fadawa manema labaru cewa, Mamora ne aka fara ba shugaban hukumar tashohin jiregen ruwa na Najeriya (NPA) a 2016 kafin wasu manya a gwamnatin Buhari suka sa aka cire sunan sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng