Jagoran IPOB Nnmadi Kanu yana hannun Sojojin Najeriya – Opara

Jagoran IPOB Nnmadi Kanu yana hannun Sojojin Najeriya – Opara

Maxwell Opara da yake jawabi a Birnin Tarayya Abuja yace Jami’an Sojoji sun san inda Nnamdi Kanu take. Lauyan yace Jami’an Sojojin ne su ke rike da Nnamadi Kanu a hannun su.

Wani babban Lauya mai kare hakkin Bil-Adama a Najeriya Maxwell Opara ya tubure cewa Sojojin Najeriya sun san inda Jagoran Kungiyar Biyafara na IPOB Nnamdi Kanu ya ke.

Jagoran IPOB Nnmadi Kanu yana hannun Sojojin Najeriya – Opara
Jagoran Kungiyar IPOB Nnmadi Mazi Kanu a cikin Kotu

Babban Lauyan kasar Opara yace Gwamnatin Tarayya tayi daidai da ta shigar da Nnamdi Kanu kara a Kotu bayan da ya saba sharudan belin da aka ba shi. Daga baya dai Gwamnati ta nemi Kotu ta janye belin da ta ba Nnamdi Kanu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya halarci daurin auren Iyalin Dangote

A lokacin da ake shirin zama a Kotu ne cikin watan Satumba Sojojin Najeriya su ka shiga gidan Nnamdi Kanu inda su ka hallaka Jama’a. Bayan nan kuma Sojojin sun kara komawa gidan inda su ka kashe mutane 28 su ka tafi da gawar.

Lauyan da ke kare hakkin marasa galihu yace tun bayan da Sojoji su ka kai hari a gidan na Nnamdi Kanu, ba a kara jin labarin sa ba. Yanzu dai wani Sanata a Yankin Enyinnaya Abaribe ya maka Gwamnati kotu inda yace ta fito da Kanu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng