Ruwan bama-bamai: Al'ummar wasu kauyuka a jihar Adamawa zasu maka sojin sama a kotun ICC

Ruwan bama-bamai: Al'ummar wasu kauyuka a jihar Adamawa zasu maka sojin sama a kotun ICC

- Al'ummar kabilar Bachama dake karamar hukumar Numan a jihar Adamawa su zargi hukumar sojin sama da kashe ma su mutane

- Sun ce sojin saman sun yi ruwan bama-bamai a wasu kauyukan su guda shida tare da bayyana cewar zasu shigar da dakarun sojin kara a kotun hukunta laifukan ta'addanci ta ICC

- Darekta yada labarai a hukumar sojin sama, Olatokunbo Adesanya, ya karyata rahoton cewar su ne su ka lalata kauyukan

Al'ummar kabilar Bachama dake zaune a wasu kauyuka shida dake jihar Adamawa sun zargi sojin saman Najeriya da yin ruwan bama-bamai a kan kauyukan su.

Al'ummar kauyukan sun bayyana cewar za su shigar da karar hukumar sojin saman a gaban kotun hukunta laifukan ta'addanci ta duniya (ICC).

Ruwan bama-bamai: Al'ummar wasu kauyuka a jihar Adamawa zasu maka sojin sama a kotun ICC
Ruwan bama-bamai: Al'ummar wasu kauyuka a jihar Adamawa zasu maka sojin sama a kotun ICC

Mazauna kauyukan; Lawaru, Dung, Nzoruwe, Pulum, Kudomti, da Shaforon, sun ce sojin sama sun yi ruwan bama-bamai a kan kauyukan su ranar 4 ga watan Disamba, 2017, yayin wani rikici tsakanin mazauna kauyukan da makiyaya.

KU KARANTA: Gwamna Bello ya yi zazzaga, ya sauke dukkan masu mukaman siyasa a jihar Kogi

A wata sanarwa da sakataren hadakar kungiyar mazauna kauyukan, Lawrence Jonathan, ya karanta mwa manema labarai, ya ce dakarun sojin sun yi yunkurin share kabilar Bachama daga doron kasa a saboda haka zasu shigar da kara domin neman hakkin su.

Sai dai, darektan hulda da jama'a na hukumar sojin sama, Olatokunbo Adesanya, ya musanta wannan zargi tare da yin watsi da rahoton cewar jiragen yakin hukumar sun yi ruwan wuta a kauyuka biyar dake yankin karamar hukumar Numan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng