Shugaba Buhari ya daga kofin duniya a babban birnin tarayya

Shugaba Buhari ya daga kofin duniya a babban birnin tarayya

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa hukumar kwallon kafa ta Duniya ta gabatarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kofin duniya wanda za a lashe a gasar cin kofin duniya ta wannan shekara a kasar Rasha.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da zasu kara a gasar, sannan a dazu kofin ya iso kasar.

Jirgin kamfanin Coca-Cola ne ya kawo tawagar mutanen dake dauke da kofin inda ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Shugaba Buhari ya daga kofin duniya a babban birnin tarayya
Shugaba Buhari ya daga kofin duniya a babban birnin tarayya

Ministan wasanni da matasa Barista Solomon Dalung, ya ce wannan tamkar lasawa Najeriya zuma a baki ne a lashe, "saboda haka babu shakka mu ne za mu shanye zumar nan."

KU KARANTA KUMA: Harin bom – Kotu ta yanke wa Charles Okah hukuncin daurin rai da rai

Shugaba Buhari dai ya lashi takobin bayar da cikakken goyon baya ga 'yan wasan kasar don ganin sun samu nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel