Marmari daga nesa: Za a fara horas da sababbin Sojojin saman Najeriya da aka a dauka

Marmari daga nesa: Za a fara horas da sababbin Sojojin saman Najeriya da aka a dauka

- Za a fara horar da Sojojin saman kasar nan da aka dauka aiki a baya

- Wadanda su ka samu Sojan sama cikin jerin kwanaki za su fara aiki

- Za a horar da sababbin Sojojin ne a gidan Sojan sama da ke Kaduna

Mun samu labari cewa lokacin da za a fara horas da sababbin Sojojin saman da aka dauka a Najeriya ya zo. Yanzu haka dai Rundunar Sojin kasar tayi jawabi.

Za a fara horas da sababbin Sojojin saman Najeriya da aka a dauka
An dauki sababbin Sojojin sama aiki a Najeriya

A dazu ne mu ka samu labari cewa Rundunar Sojojin sama na kasar ta bayyana cewa wadanda su ka samu dacewa da shiga gidan Sojojin saman kasar su fara shiryawa horas da su da za ayi a Ranar Alhamis na mako mai zuwa.

KU KARANTA: An bude wani sabon barikin Soji a Jihar Bayelsa

Ana sa rai sababbin Sojojin kasar da aka dauka su hallara a filin daukar sababbin Jami’ai na Makarantar horar da Sojojin kasar da ke cikin gidan Sojojin saman Najeriya a Unguwar Kawo da ke cikin Garin Kaduna a Jihar.

Darektan yada labarai na gidan Sojan sama na kasar Air Vice Marshall Olatokunbo Adesanya ya bada wannan cikakken jawabi ta shafin su na Facebook dazu. Zuwa 15 ga watan nan na Maris ake sa rai a fara horar da Sojojin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng