YouWin: Gwamnatin Buhari tayi wa Matasa alkawari ba ta cika ba

YouWin: Gwamnatin Buhari tayi wa Matasa alkawari ba ta cika ba

- Gwamnatin Buhari ta raya tsarin YouWin na mulkin Shugaba Jonathan

- An yi wa Matasan da su ka ci jarrabawar alkawarin jari domin kasuwanci

- Sai dai wasu sun ci jarrabawar amma an hana su wannan kudi har yanzu

Mun samu labari na musamman cewa wadanda su ka nemi jarin kasuwanci ta tsarin YouWin Connect na Gwamnatin Shugaba Buhari sun koka da cewa akwai rashin gaskiya a lamarin. Ibrahim Musa ya bayyana mana yadda abin yake.

YouWin: Gwamnatin Buhari tayi Matasa alkawari ba ta cika ba
Masu neman jarin You Win sun koka a Najeriya

A lokacin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne aka kirkiro You Win wanda Shugaba Buhari ya cigaba da tsarin amma ya canza masa suna zuwa YouWin connect inda aka yi alkawarin raba sama da Naira Biliyan 10 ga Matasa.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya bayyana nadamar sa

An kawo tsarin ne ga Matasa 61, 000 da ke kokarin kasuwanci musamman a harkar noma da ilmin zamani na sadarwa da sauran su. Sai dai wasu sun bayyana mana cewa sun yi duk abin da ake bukata amma Gwamnati ta yaudare su.

Wannan Bawan Allah Ibrahim ya bayyana mana cewa ya lashe duk jarrabawar da ake yi amma aka sauya sunan sa da na wani dabam. Ibrahim yace a sakamakon da aka fitar yana cikin wadanda su ka fi kowa kokari amma aka yi watsi da shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng