Dattawan Kwankwaso sunyi Allah wadai da furucin Rabiu Kwankwaso kan auren yar Ganduje
- Dattawan Kwankwaso sunyi Allah wadai da furucin Rabiu Kwankwaso kan auren yar Ganduje
- A cewarsu kalaman Kwankwaso ya bar bangaren siyasa ya shafi martaba da alfarman aure
- Kwankwaso dai yace mutane sun bata lokacinsu wajen halartan auren zawarawa
Rahotanni sun kawo cewa dattawan yankin Kwankwaso dake karamar hukumar Madobi na jihar Kano sun nuna bacin ransu akan furucin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso game da auren yar gwamnan jihar Kano, Fatima Ganduje.
Inda sukayi Allah wadai da lakabi da yayi wa auren na cewa auren zawarawa ne.
A wani taron gaggawa da dattawan suka gabatar karkashin jagorancin mahaifin tsohon gwamnan, wanda shine Hakimin Madobi, Dattijo Musa Kwankwaso, dattawan sun nuna bacin rai kan yadda Kwankwaso ya fita daga da'irar siyasa ya koma ga batanci ga alfarmar aure gami da mutuntaka ta gwamnan Kano Ganduje.
Wata majiya wacce ba ta so a bayyana sunanta ba ta bayyanawa manema labarai cewa, ana zargin cewa an ma bugawa tsohon gwamnan waya a wajen taron, kuma a ka bude kowa yana jin maganarsa da a kai wayar.
An kuma tattaro cewa a lokacin da aka sanar da shi cewar an kira shi ne saboda a nuna bakin cikin dattawan garinsu na Kwankwaso gami da rokon da suke masa kan ya yi ta maza ya janye maganar batanci da ya yi akan auren yar gwamna Ganduje, sai ya kashe wayarsa.
Bayan nan kuma ana zargin cewa an buga masa waya ya fi sau goma sha biyar amma ya ki amasawa. An aika masa kuma da sakon waya sau goma amma bai amsa ko daya ba.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kwankwaso yayi ba’a ga ma’auratan, cewa ‘zawarawa’ne.
Ya kuma bayyana cewa manyan masu ruwa da tsaki da suka bar gurin aikinsu don halartan bikin basu da aiki a gabansu.
KU KARANTA KUMA: 2019: Wani babban 'Dan APC ya roki Shugaba Buhari ya karasa ladan sa
“Mun kuma samu labarin cewa mutane daga gurare da dama da basu da aiki a gabansu sun bar ayyukansu domin halartan bikin.
“Na kuma samu labarin cewa wannan biki na mutun daya ya dakatar da mutane daga gudanar da harkokinsu. "
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng