Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Taraba yau

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Taraba yau

Bisa ga kasha-kashe da ya faru a jihar Taraba karshen makon da ya gabata, ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyarar ban mamaki jihar Taraba yau.

Jaridar Vanguard ta bada wannan rahoto ne da safiyar yau Litinin, 5 ga watan Maris, 2018. Wannan labari na fitowa ne bayan ana sa ran shugaban kasan zai je kasar Ghana domin halartan taron murnan zagayowar ranan samun yanzin kasar shekari 61.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan ne a shafin sada ra'ayi da zumuntarsa na Facebook da daren jiya Lahadi.

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Taraba yau

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Taraba yau

Jama'a na ganin cewa Buhari ya amsa kukan jama'a ne bayan jama'a masoya da yan adawarsa suka caccakesa akan cewa ya halarci auren diyar gwamnan jihar Kano amma yayi kunnen kashi da kiran mutane cewa ya ziyarci iyayen yan matan Dapchi da kisan Mambila.

KU KARANTA: Anyiwa shugaba Buhari rasuwa

Wasu sun kara da cewa da alamun ba shugaba Buhari ke mulki ba saboda bai iya zuwa inda ya ga dama lokacin da ya ga dama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel