Jam'iyyar APC ta lashe kananan Hukumomi 7 a zaben Jihar Edo

Jam'iyyar APC ta lashe kananan Hukumomi 7 a zaben Jihar Edo

- Jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zaben Jihar Edo

- PDP ta kauracewa zaben kananan Hukumomin da aka yi jiya

- Har yanzu ba a kammala bayyana sakamakon zaben ba tukun

Mun samu labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki tayi wa Jam’iyyar adawa ta PDP dukan babban-bargo a zaben kananan Hukumomin da aka yi a Jihar Edo. Jam’iyyar ta APC mai mulki a Jihar ta lashe zaben kananan Hukomi 7. Yau aka cigaba da kirga kuri’un.

Jam'iyyar APC ta lashe kananan Hukumomi 7 a zaben Jihar Edo
APC ta cinye kananan Hukumomi a zaben Jihar Edo

Sakamakon zaben da mu ka samu daga Hukumar zabe ta Jihar EDSIEC ya nuna cewa APC ta samu gagarumar nasara a zaben da aka yi wanda Jam’iyyar adawa ta PDP ta kauracewa. Farfesa Stanley Orobator ya bayyana wannan bayan an kirga kuri’un zaben.

KU KARANTA: Rikicin cikin gidan Jam’iyyar APC yayi kamari a Jihar Kogi

Jami’in zaben ya sanar da cewa Oteh Omoru ne yayi nasara a karamar Hukumar Akoko-Edo. A Karamar Hukumar Ovia kuwa, Destiny Enabulele ne yayi nasara da kuri’u 56,664. A Makwabta Ovia ta Arewa maso gabas kuma Ogbemudia Osaze ne yayi nasara,

A sauran kananan Hukumomin ma dai irin su Uhunwode, Egor, da Yammacin Owan, duk Jam’iyyar ta APC ce tayi nasara da kuri’un da su ka ribanya na sauran Jam’iyyun da su kayi takara irin su SDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng