Za'a hukunta masu yadda kalaman kiyaya ta hanyar rataye - Majalisar Dattawa

Za'a hukunta masu yadda kalaman kiyaya ta hanyar rataye - Majalisar Dattawa

- Majalisar Dattawa ta gabatar da wani kudirin da ke bukatar a yanke hukuncin kisa ta hanyar rataye ga duk wanda aka samu da laifin yadda kalaman kiyaya

- Kudirin kuma ta bukaci gwamnati ta kafa Hukumar yadda kalaman kiyaya na kasa da zai yi hani kan yadda kalaman battanci da ke haifar da fitina a kasa

- Ana sa ran kafa hukumar zai rage banbance-banbance da ake nuna wa al'umma bisa yare, jinsi ko kuma addini

Majalisar dattawa ta gabatar da sabon kudirin kafa dokar hana yada kalaman kiyaya inda ta bukaci yanke hukuncin kisa ta hanyar rataye ga duk wanda aka samu laifin yadda kalaman da sukayi sanadiyar rasa rai/rayyuka.

Kudirin da mai magana da yawun Majalisar, Sanata Aliyu Sabi ya gabatar ana sa ran zai kawo karshen yadda kalaman kiyaya da al'umma ke yadawa barkatai wanda hakan ke haifar da fitinu daban-daban.

Za'a hukunta masu yadda kalaman kiyaya ta hanyar rataye - Majalisar Dattawa
Za'a hukunta masu yadda kalaman kiyaya ta hanyar rataye - Majalisar Dattawa

Har ila yau, kudirin ta bukaci gwamnatin tarayya ta kafa hukumar hana yadda kalaman kiyaya na kasa wanda za tayi hani ga yadda kalaman batancin.

KU KARANTA: Kudurin kirkirar Peace Corps: Majalisar wakilai ta yi alla-wadai da kin amincewar Buhari

Kudirin kuma ya bukaci a yanke hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar ko sama da haka ko kuma tarar naira miliyan 10 ga duk wanda aka samu da laifin cin zarafin wani bisa banbancin kabilanci ko jinsi.

Hukumar za ta bullo da shirye-shiryen da za su kawo hadin kai da zaman lafiya tsakanin al'umma daga kabilu da addinai daban-daban.

Hakazalika, kafa hukumar zai haifar mutunta addinai ta al'addun al'ummar Najeriya daga kowane yanki na kasar nan. Kuma zai bawa kowa damar amfana da ababen more rayuwa da gwamnati ta samar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164