2019: Tsohon Shugaban ICAN Chidi Ajagebu ya bar Jam'iyyar APC
- Wani babba a da a APC ya tsere zuwa Jam’iyyar APGA
- Ajaegebu yace APGA ce ta dace da Inyamuran Najeriya
- ‘Dan siyasar zai kuma nemi kujerar Sanata a zaben 2019
Jam’iyyar APC mai mulki tayi babbar asara bayan da Chidi Ajaegebu wanda a da yana cikin manya a tafiyar Jam’iyyar ya zare kafafun sa ya koma Jam’iyyar APGA wanda yace ita ce ke da manufofin kawo gyara a Kasar Inyamurai.

Chidi Ajagebu wanda shi ne Shugaban Kungiyar akawun Najeriya a wani lokaci ya bayyana cewa Jihar Abiya tana cikin wadanda su ka fi kowa ci-baya a Najeriya saboda mugun mulkin Jam’iyyar PDP don haka bai koma Jam'iyyar ba.
KU KARANTA: Ashe Jonathan bai taba niyyar zama Mataimakin Shugaban kasa ba
Ajagebu ya koka da yadda Jihar ta Abiya ta zama kashin-baya a Kasarduk da irin albarkatun da ta ke da shi. Tsohon Shugaban na ICAN yayi wannan jawabi ne a Hedikwatar Jam’iyyar APGA da ke Garin Umahia a Jihar ta Abiya.
Babban Akantan ya kuma fito da shirin sa a fili inda yace zai nemi kujerar Sanatan Yankin Jihar Abia ta tsakiya a zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar sa ta APGA. Ajagebu yace duk wani Inyamuri a gida da waje akwai jinin APGA a jikin sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng