Bayan ya share shekaru biyar a kasar waje, matarsa ta ki kwanciya dashi
- Auren nasu ya shekara goma sha uku
- Ta ce sai yayi gwajin kanjamau sannan zata sadu dashi
- A kasashen waje dai, saduwa ta yawaita saboda rashin ta-ido
Tsoron kanjamau da ma sauran cututtuka da ake sammu yayin saduwa ya sanya wata mata kin saduwa da mijinta wai sai yayi gwaji, batu da ya tayar da taqaddama a cikin gidansu na aure. Ita dai tace tana da hujjar cewa maigidanta yayi mu'amala da matan banza, zargi da yace zagi da raini ne.
Ita dai tana ganin ba yadda za'ayi ya shekara biyar a kasar waje, ba tare da ace yayi mu'amala da wasu matan ba. Shi kuwa gogan naka, ya kafe shi babu wani gwaji da za'ayi, wai ai shi mutumun kirki ne.
Shi dai Mr. Ayoro da ke auren matarsa Betty, wadda suka shafe shekaru 13 da aure, wanda ya basu yara har ukku, yayi bulaguro neman arziki inda ya fara yawon duniya, ya kuma shafe shekaru biyar bai zo gida ba.
DUBA WANNAN: Wani saurayi na zargin matarsa da cikin shege
A rigimar da suka fara a cikin gida dai, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, abu ya kacame an bar Legas an koma kautye na Anambara domin ko dattijai zasu iya shawo ka wannan lamari.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng