An bankado mabuyar Femi Fani-Kayode bayan yayi wa Kotu karyar rashin lafiya

An bankado mabuyar Femi Fani-Kayode bayan yayi wa Kotu karyar rashin lafiya

- Ashe Gwamnan Ekiti Ayodele Fayose ne ya boye Femi Fani-Kayode

- Wasu sun ce Mr. Femi Fani Kayode yana gidan Gwamnan Jihar Ekiti

- Yanzu haka dai ana neman tsohon Ministan kasar a Kotu ruwa a jallo

Mun fara jin kishin-kishin din cewa Femi Fani-Kayode yana wasan buya yanzu da Hukuma. Yanzu haka dai tsohon Ministan ya fadawa Kotu inda ake neman sa cewa yana fama da matsalar ciwon zuciya.

An bankado mabuyar Femi Fani-Kayode bayan yayi wa Kotu karyar rashin lafiya
Gwamna Fayose ne ya boye Femi Fani-Kayode

Jaridar Sahara Reporters tace yanzu haka Femi Fani-Kayode yana Jihar Ekiti. Majiyar tace Gwannan na boye ne a bangaren Gwanana a cikin gidan Gwamnatin na Jihar Ekiti inda yake gudun ayi ram da shi. Ba mamaki DSS ta taso shi gaba.

KU KARANTA: Gwamnan Benuwe zai koma Jam'iyyar PDP

Tsohon Ministan al'adu da kuma safarar jirgin sama na kasar a lokacin mulkin Obasanjo yana tsoron Jami'an tsaro su yi wasan kura da shi saboda irin sukar Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yake yi dare da rana.

Mista Fani Kayode ba zai so a tsare sa kamar yadda Gwamnatin kasar ta yi wa Sambo Dasuki kamun babban bargo ba. Ana dai shari'a da Kayode inda ake zargin sa da yin sama sa fadi da wasu kudi. Yanzu dai ya fadawa Kotu bai da lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: