An kama likitan bogi a jihar Nasarawa
- An kama wani likitan bogi a jihar Nasarawa
- An kama shi da laifin bawa mata maganin daukar ciki
- Hukumar NAPTIP zata gurfanar dashi a gaban kotu nan ba da dadewa
Hukumar yaki da safarar mutane ta kasa, Naptip ta damke Dr Akuchi ne a 'yan makonnin da suka wuce bisa zarginsa da taimaka wa mata samun ciki na bogi daga bisani kuma ya basu jarirai.
Jami'an hukumar sun zargi likitan gargajiyan da yi wa mata 160 maganin samun ciki na bogi a tsawon shekaru hudu da ya yi yana wannan aiki a wani asibiti da ke jihar Nassarawa.
Wasu daga cikin matan sun shaidawa majiyarmu cewar mutumin ya karbi makudan kudade daga hannunsu.
DUBA WANNAN: Wasu Sanatoci sun nuna rashin amincewar su game da sauya tsarin zabe da majalisar datijjai ta yi
Hukumar ta NAPTIP ta ce nan bada jimawa ba zata gurafar da Dr Akuchi a gaban kotu.
Yankin kudu mo gabashin Nigeria dai ya yi kaurin suna wajan safarar jarirai, inda ko shekarar 2011 yan sanda suka kai samame a wani gida da ke Aba a jihar Abia inda suka gano yan mata fiye da 30 wadanda ake zargin ana yi mu su ciki domin su sayar da jariransu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng