An yankewa matashi dan Boko Haram mai suna Sunday Abana shekaru 40 a gidan yari
Babban kotun tarayya da ke zaune a barikin Wawa, Kainji jihar Neja, a ranan Alhamis ta yankewa Sunday Abana shekaru 40 a gidan maza domin kasancewa dan Boko Haram kuma ya kai hare-hare wurare daban-daban a jihar Borno a shekarar 2015.
Sunday Abana dan karamar hukumar Asikra Uba ne a jihar Borno wanda ya taimaka wajen kai hare-hare kungiyar a shekarar 2013.
Kana an yankewa wani matashi Babagana Ali shekaru 25 a gidan yari bisa ga gudunmuwarsa a hare-haren da kungiyar ta kai a shekaran 2015.
Abana ya yi amanna da dukkan laifin da akayi zarginsa da shi inda yace a horar da shi a cikin daji ne.
KU KARANTA: Shugaba Buhari zai gana da gwamnonin APC a garin Daura
Ya bayyana cewa yanada hannu cikin wasu hare-hare da aka kai kauyuka 8 inda akayi asaran rayuka da dama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng