Gwamnonin Arewa za su iya magance rikicin makiyaya da manoma - Inji Aminu Masari
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ja hankalin gwamnonin Arewa 19 da su kirkiri wani tsari na bai-daya da zai iya kawo karshen rikicin makiyaya da manoma.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a yayin da sabon shugaban kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa, na jihar Katsina, Abdulhamid Sabo ya kai masa ziyara.
Masari ya yi wannan jawabin ne kwanaki kadan bayan da gwamnan jihar Kano ya gayyaci daukacin makiyayan da ke Arewa su yi kaura daga duk inda su ke su koma jihar Kano, domin akwai yalwar wurin kiwo a jihar.
Ya jadadda cewa gwamnoni na da dama da kuma hanyoyin magance wannan mummunar kashe-kashe da ake yawan yi a rikicin makiyaya da manoma.
Ya ce yankin Arewa na da fadin kasa da yalwar wuraren kiwo, maimakon makiyayan nan su rika gallafiri daga nan zuwa can ana haddasa kashe-kashe.
KU KARANTA KUMA: Bance a zabtare albashin yan majalisa ba – Sarki Sanusi
Ya ce su dawo yankin Arewa su zauna, sannan za a gina musu makarantu da sauran ababen more rayuwa kuma shanun su za su yi kiwo cikin walwala.
A wani al'amari na daban, Legit.ng ta ruwaito cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya karyata zarge-zagen cewa yayi kira ga zabtare albashin yan majalisar dokokin kasar.
Sanusi, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa daga babban ma’aikacinsa, Munnir Sanusi, yace sanarwan da akayi da sunansa karya ne, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng