Ana samar da megawatt 94,627 na lantarki a kullum cikin watanni 4 na karshen shekarar 2017 - NBS
- Hukumar Kididdiga na kasa (NBS) ta fitar da bayanai kan adaddin lantarki da tashoshin samar da wutan lantarki na Najeriya suka samar watanni 4 na 2017
- Rahoton kuma ya bayyana ranakun da tashoshin sukafi samar da lantarkin da kuma ranakun da ba'a samu lantarkin sosai ba
- Har ila yau, rahoton ya bayyana adadin abokan huldar kamfanin wutan lantarkin da ke amfani da na'urar mita da adadin wanda ba su da mitar
Tashoshin Samar da wutan lantarkin na kasa suna samar da megawatt 94,627 na wuta a kowane rana cikin watanni hudu na karshen shekarar 2017 inji wani rahoto da ya fito daga Hukumar Kididdiga na Kasa (NBS).
Kamar yadda bayanai da hukumar kididigar da bayar a shafin ta na yanar gizo a ranar Alhamis, adaddin wutan lantarkin mafi girma da aka samar shine megawatt 105,152 a ranar 8 ga watan Disambar bara kuma mafi karanci shine magawatt 73,246 a ranar 18 ga watan Oktoban 2017.
KU KARANTA: Karancin man fetur: Lamarin na kara tsananta a Abuja da ma wasu johohin
A rahoton da ke bayyana adadin wutan lantarkin da tashoshin wutan suka samar da kuma adadin da al'umma sukayi amfani da shi. Rahoton ya nuna cewa tashohin samar da lantarki masu amfani da ruwa sun samar da mega watt 21,126, sauran tashohin da ba na ruwa ba kuma sun samar da megawatt 84,026.
Rahoton kuma ya bayyana cewa abokan huldar hukumar samar da lantarkin guda miliyan 3.45 ne ke amfani da na'urar mita mai lissafa adadin wutar da ake amfani dashi cikin masu hulda guda miliyan 7.48 da hukumar ke dashi.
Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa masu amfani da lantarki na garin Benin ne ke kan gaba wajen amfani da mita sai garin Eko ke biye da su sannan Ikeja. Yola da Enugu ne sukafi karancin masu amfani da na'urar mitar.
A baya, Legit.ng ta kawo ruwaito muku yadda akayi asarar wutan lantarki mega watt 16,729 cikin kwanki bakwai bisa tangarda da aka samu da na'urar karbar wutan lantarkin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng